26 Afirilu 2021 - 13:05
Iran : Zarif, Ya Isa Iraki, Bayan Kammala Ziyara A Qatar

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya isa birnin Bagadaza na kasar Iraki, da sanyin safiyar yau Litini, a ziyarar da ya ke a yankin.

ABNA24 : Yayin ziyarar tasa ta kwanaki biyu, Zarif, zai gana da takwaransa na Iraki, da kuma wasu jami’an kasar.

An kuma tsara Zarif, zai gana da mahukuntan yankin Kurdistan na Irakin.

Tunda farko dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ya bayyana a jiya cewa, ziyarar ta Zarif, za ta maida hankali kan huldar dake tsakanin kasashen biyu makobtan juna.

Ziyarar ta ministan harkokin wajen kasar ta Iran, na zuwa ce bayan wacce ya kammala a kasar Qatar, inda cen din ma suka tattauna kan batutuwan da suka shafi alakar dake kasashen biyu da kuma tattaunawa da ake game da farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran.

 

342/